7 Oktoba 2021 - 11:03
​Bankin Duniya: Tattalin Arzikin Yankin Kudu Da Sahara Zai Habbaka Da Kashi 3.3% A Wannan Shekara

Rahoton bankin duniya ya ce, tattalin arzikin yankin kudu da Saharar Afirka zai haɓaka da 3.3% a wannan shekarar, sannan kuma zai kai kashi 3.5% a shekarar 2022: Bankin Duniya

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : Rahoton ya ce, a bisa binciken ma’aunai na habbakar tattalin arziki da aka yi la’akari da su, ana sa ran tattalin arzikin yankin kudu da Sahara zai bunkasa da kashi 3.3% a wannan shekarar da kashi 3.5% a shekarar 2022.

Rahoton wanda aka fitar a yau Laraba, ya yi ishara da hauhawar kayan masarufi da aka samu musamman ma saboda wasu ka’idoji da suka suka kawo tsaiko a harkokin kasuwanci domin dakile yaduwar cutar corona, amma bisa la’akari da yadda aka fara samun farfadowa a wasu bangarorin a halin yanzu, wannan yasa tattalin arziki kasashen wadannan yankuna ya fara murmurewa.

Rahoton Bankin Duniya ya ce ci gaban zai iya zama mafi girma idan ya kai 5.1% a cikin shekarar 2022, wannan kuwa zai iya faruwa ne idan aka samu nasarar yin allurar rigafin cutar corona cikin sauri, wanda kuma duk wani tsaiko da za a samu dangane da hakan, zai iya kawo cikas ga hasashen da ake yin a ci gaban tattalin arzikin yankin.

342/